Bidiyo: Yanda tsohuwar matar Ado Gwanja ta cashe akan wakar tsohon mijin ta.

Lallai wannan shi ake kira “Abu namu maganin a kwabe mu” tsohuwar matar mawaki kuma jarumi Ado Gwanja wato Maimuna, itama ta fito ta wataya akan wakar tsohon mijin ta, kamar yanda sauran ‘yan mata suke yi.

A cikin satin nan ne dai Ado Gwanja ya saki sabuwar wakar tasa mai taken “Warr” wadda a yanzu yan mata suke ta fitowa suna taka rawa akan wakar, akan shafukan sadarwa.

To itama dai Maimunan Gwanja tace baza’a barta a baya ba, duk da cewa yanzu babu aure tsakanin ta Gwanjan, amma kuma ta tayashi tallata wakar tasa.

Bari dai kuga bidiyon, kamar yanda ta cashe da wakar tsohon mijin nata.