Bidiyo: Wani matashi ya sadaukar da azumin sa na Arfa, zuwa ga Maryam Yahaya saboda soyayyar da yake mata.

Wani matashi ‘dan soyayya mai suna El Shanawa ya bayyana wani al’amari da ya ‘daure wa mutane kai, inda ya fito ya fada cewa Azumin da yayi na ranar Arfa ya sadaukar dashi kacokan ga jaruma Maryam Yahaya.

Lallai wannan soyayyar ta daban ce, domin wasu ma suna ganin babu komai a cikin ta sai hauka da kuma rashin hankali, domin kuwa abin ya wuce gona da iri.

To shi dai dama wannan matashi yayi ‘kaurin suna akan Soyayyar Maryam Yahaya, domin kuwa yayi abubuwan mamaki iri daban-daban akan soyayyar.

Yanzu dai bari kuji, ku kuma gane wa idanun ku yanda wannan matashi yake masifar ‘kaunar jaruma Maryam Yahaya.

Ga bidiyon nan a kasa, daga tashar Duniyar Kannywood.