Bidiyo: Abinda ya faru a Kotun ‘daukaka ‘kara, dangane da shara’ar Abduljbbar.

Har yanzu dai tsugune bata ‘kare ba akan shara’ar shek Abduljbbar shek Nasiru Kabara, wadda Gwamnatin Kano ta maka shi a Kotu, bisa zargin yin kalaman ‘batanci akan Manzon Allah SAW.

Bayan malamin tare da lauyan sa sun gamsu, kuma sun hada baki akan cewa Kotun da take jarogantar Shara’ar baza yi musu adalci ba. Wannan kuma dalilin da yasa suka tafi Kotun ‘daukaka ‘kara kamar yanda Doka ta basu dama.

Lauyan na Abduljbbar yayi bayani a takaice, dangane da abinda ya faru a Kotun ‘daukaka ‘karar. Ga kuma abinda yake cewa.