Bidiyo: Amarya ta koma ga Allah, ana saura kwana 15 auren ta.

Allahu Akbar wata amarya mai suna Rukayya Ibrahim ‘yar jihar Bauchi ta rigamu gidan gaskiya, a lokacin da ake gaf da ‘daura mata aure.

Kana taka Allah na Tasa, kuma a koda yaushe ta Allah itace gaskiya. “Kullu nafsin za’ikatul mauti”, wannan magana haka take, sannan kuma babu wanda ya san ranar mutuwar sa, da kuma abinda zaiyi sanadiyyar barin sa duniya. Wannan wani Ilimi ne, wanda Allah Shi kadai Ya bar wa kanSa sani.

Ita dai Rukayya, Allah Ya riga Ya ‘kaddara mata cewa zata bar duniya, ba tare da tayi aure ba, domin kuwa a lokacin da ta rasu, gaba ‘daya kwana 15 suka rage ta zama amarya.

Ga dai takaitaccen rahoto nan a ‘kasa, daga tashar Kundin Shahara.