Bidiyo: Iyayen Hanifa sun sake yin magana a karo na 2, bayan hukuncin kisa da aka yanke wa Abdulmalik.

Iyayen marigayiya Hanifa sun kuma yin magana a karo na biyu, bayan hukuncin da Kotu ta yanke akan makasan yarinyar, wato Abdulmalik da Hashim da kuma Fatima.

Baban Hanifa ya bayyana farin cikin sa da jin dadin sa akan hukuncin kisa ta hanyar rataya da Kotu ta tabbatar akan Abdulmalik Tanko, inda za’a zartar masa da hukuncin bayan ya gama zaman shekaru 5 a Kurkuku.

Su kuma sauran da suka taimaka masa aka yanke musu hukuncin ‘daurin shekaru 2, wanda su idan sun gama zaman su zasu koma gida.

Ga dai bayanin daga bakin Mahaifin marigayiyar.