Bidiyo: Safara’u tana shirin fitar da sabuwar waka ta ‘daukar magana.

Safara’u Kwana 90, wadda tace ta bar sana’ar fim ta koma waka, yanzu ta gama shiryawa tsaf, domin fitar da sabuwar wakar ta, tare da abokin aikin ta wato Mr. 442.

To ita dai Safara’u wata sabuwar mawakiya ce, wadda ta ‘dauki wani salo na yin wakokin iskanci da batsa, inda a haka take ta tara masoyan ta da mabiyan ta a shafukan sada zumunta.

Sai dai Safara’u tafi samun karbuwa a shafin Tiktok, domin kuwa ta nan ne akafi sanin ta a wakokin nata na iskanci da fitsara.

Yanzu dai bari kuga kadan daga cikin wakar da Safan take shirin fitarwa.