Bidiyo: An kori ‘Dan sandan Nigeria daga aiki, saboda karbar cin hanci.

Wani Dan sanda a Najeriya yaci taliyar ‘karshe, inda aka kore shi daga hukumar su, a bisa laifin karbar cin hanci a hannun mutane.

‘Dan sandan mai suna Richard Gele, an kama shi Dumu-dumu akan babban titi, yana ‘kokarin karbar cin hanci. Kuma yana nuna cewa wannan harkar itace sana’ar sa.

To kusan dai zamu iya cewa an tambara jami’an tsaron Najeriya akan wannan ‘dabi’a ta karbar cin hanci da rashawa, musamman ma kuma hukumar ‘yan sanda.

Bari dai yanzu kuga cikakken rahoton yanda aka kama wannan ‘dan sanda kuma aka sallame shi daga aiki. Gashi nan a ‘kasa.