Bidiyo: Mr. 442 mai gidan Safara’u ya fusata saboda ana musu kallon ‘yan isa.

Mr. 442 wato abokin aikin Safara’u, ta wani ‘bangaren kuma mai gidan ta, yayi zazzafan martani a cikin tsananin fushi, akan masu kallon su a matsayin ‘yan iska masu ‘bata tarbiyya.

Ita dai Safara’u da mai gidan nata sun kasance suna yin wakokin batsa da kuma yin kalaman iskanci a cikin wakokin su. Sai dai suna ganin wannan ba komai bane face neman halak ‘din su.

Ga dai bidiyon nan a ‘kasa, wanda 442 yake ta balbalin bala’i akan masu ce musu ‘yan iska kuma masu lalata tarbiyyar al’umma.