Bidiyo: Za’aci gaba da gudanar da karatu, a makarantar da aka kashe Deborah.

Daga ‘karshe dai Gwamnatin jihar Sokoto ‘karkashin jagorancin Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ta fara shirye-shiryen bude makarantar Kwalejin Ilimi ta jihar wato Shehu Shagari, inda aka kashe Deborah Samuel.

Makarantar dai tana nan har yanzu a garkame tun bayan abinda ya faru da dalibar da ta zagi fiyayyen halitta SAW, wanda hakan yasa wasu matasa ‘yan makarantar suka kashe ta, ta hanyar banka mata wuta.

A lokacin da wannan al’amari ya faru, duk duniya babu inda labarin bai shiga ba, har sai da ya kusa haddasa yaki tsakanin Musulmai da Kiristoci.

To yanzu dai an fara tunanin bude makarantar aci gaba da karatu kamar yanda aka saba.

Ga kuma cikakken rahoto nan a ‘kasa, akan wannan magana.