Labaran Kannywood

Bidiyo: Tunda nake a Kannywood ba’a taba biyana kudin aiki kamar yanda aka biya ni a fim ‘din ‘Dan Jarida ba. Inji Kumurci.

Fitaccen jarumin Kannywood wanda ya saba fitowa a ‘bangaren ‘yan daba wato Shu’aibu Lawan Kumurci, yace tunda yake a masana’antar Kannywood ba’a taba bashi kudin aiki masu gwabi, kamar wanda Abubakar Bashir Maishadda ya bashi a sabon fim ‘din da ake ‘dauka yanzu na ‘Dan Jarida ba.

‘Dan Jarida dai wani sabon fim ne mai dogon zango wanda ake ‘daukar aikin sa yanzu. Kuma shine na farko a Kamfanin shirya fina-finai na Maishadda, wato Maishadda Global Resources.

Fim ‘din ya haska cewa akan harkar ‘yan daba aka ‘kirkire shi, domin kuwa akwai Daddy Hikima wato Abale da Na Kalala da makamantan su ciki.

Ga dai bidiyon rahoton nan a ‘kasa daga tashar Tsakar Gida, wanda Kumurci yayi waccen magana.

Related Articles

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button