Addini

Bidiyo: Yanda akayi jana’izar ‘Yan Shi’ar da aka kashe a Zaria.

‘Yan Shi’a sun gudanar da jana’izar ‘yan uwan su, wadanda jami’an tsaron Najeriya suka kashe a garin Zaria na jihar Kaduna, a ranar Ashura wadda ta gabata.

To kusan dai zamu iya cewa wannan ba shine Farau ba, wato batun rigingimun da ake samu tsakanin mabiya Addinin shi’ar da jami’an tsaro. Saboda ansha yin ba takashi a tsakanin ba sau 1 ba, ba sau 2 ba.

To yanzu ma dai an kuma, inda jami’an suka halaka ‘yan Shi’ar har mutane 6 wadanda har anyi jana’izar su. Sannan kuma sun jikkata wasu.

Lamarin kuma ya auku ne bayan sun kammala tattakin su na Ashura, kamar yanda suka saba yi duk shekara.

Ga dai bidiyon yanda jana’izar ta kasance nan a ‘kasa.

 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button