Labaran Duniya

Alhamdu Lillah, Sojojin Najeriya sun kama ‘Dan Boko Haram a Abuja.

Rundunar tsaro a Najeriya ta tabbatar da kama gawurtaccen ‘Dan Boko Haram Malam Abatcha Bukar a Abuja, babban birnin tarayyar ƙasar.

Rahoton yace, lamarin ya faru a Asokoro.

Daraktan yaɗa labarai na hukumar Manjo Bana Musa Ɗanmadami shine ya tabbatar da haka a cikin wani rahoton alƙaluman ayyukan da hukumar ra tattara daga ranar 25 ga watan Agusta zuwa ranar 8 ga watan Satumban shekarar da mu ke ciki ta 2022.

Sanarwar ta ce a tsakanin ranakun, an kashe mayaƙan Boko Haram har mutane 252 a bangaren Arewa maso gabashin ƙasar, yayin da wasu 556 da ake zargi sa shiga ƙungiyar su ka miƙa wuya.

Daga cikin waɗanda su ka miƙa wuya akwai maza su 115, sai mata 189 sai kuma yara 252.

A cikin ranakun, jami’an tsaron sun ƙwato makamai masu tarin yawa daga hannun mayakan, daga cikin makaman akwai bindigu ƙirar AK47 masu yawan gaske, sai harsashi daban-daban da baburan hawa da kuma kekuna.

Haka zalika sanarwar ta ce jami’an sun samu nasarar kubutar da ƴan matan Chibok su uku, daga cikin wadanda aka sace a shekarun baya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button