Addini

Allahu Akbar. Wasikar da Sheik Dahiru Bauchi ya tura wa Sarauniyar Ingila kafin rasuwar ta.

Wasikar Sheik Dahiru Usman Bauchi zuwa ga Queen Elizabeth (Sarauniyar Ingila) Inda kuma ya aika mata ne a cikin shekarar 2021.

Shahararren malamin addinin Islama kuma jigo a tafiyar Darikar Tijjaniyya Sheik Dahiru Usman Bauchi, ya taba aika wa marigayiya sarauniyar Ingila Queen Elizabeth wasika, kuma ya aika mata ne a cikin shekarar data gabata ta 2021, inda ya kira ta zuwa ga Addinin Musulunci.

Kuma a lokacin malamin ya rubuta wasikun ne guda 2, inda ya aika ‘dayar zuwa ga tsohon shugaban ƙasar Amurka Barack Obama, wanda a cikin wasikun, malamin ya rubuta musu cewa, ‘su musulunta su koma Addinin iyayen su da kakannin su wato ‘Addinin Musulunci” Domin duk abunda suke nema a duniya sun samu, saura lahira”. Kamar yanda Shehin malamin ya zayyana.

Itama dai a ‘bangaren ta Sarauniyar Ingila Queen Elizabeth, tasha bayyana cewa ita jikar Annabi Muhammad SAW ce, tare da ikrarin bayyana salsalar ta, har zuwa ga fiyayyen halitta Annabi Muhammad SAW.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button