Labaran Duniya

Sarauniyar Engila jikar Annabi Muhammad SAW ce. Cewar Sherif Almuhajir.

Wani bawan Allah ko kuma muce wani malami ya kawo wata magana data ba wa mutane mamaki da al’ajabi akan sarauniyar ƙasar Ingila data rasu.

A cikin bayanin bawan Allahn mai suna Sherif Almuhajir, ya tabbatar da cewa marigayiyar sarauniyar jikar Manzon Allah ce SAW.

Inda wannan malami ya karanto salsalar, wadda ta hada sarauniyar da Manzon Allah.

“Wasu masanan tarihi sun ruwaito cewa Salsalar Queen Elizabeth jikar Annabi Muhammad SAW ce, domin an gano cewa ita Jikar Za’idah ce wadda Rumawa suka sace ta, bayan sun hambare mulkin babanta mai Al-Abbad dan Muhammad Bin Abbad (Almu’tadid) wanda shine Sarki na karshe a garin Ishbiliya (Seville). Inji Sharif.

Sai kuma yaci gaba cewa, “Tarihi ya nuna cewa Zaidah ta koma hanun rumawa, inda suka kiristantar da ita suka kuma sauya mata sunan ta zuwa Izabela. Itace kuma ta auri Sarki Alfanso na hudu”.

Related Articles

3 Comments

  1. Tir Da Irin Wannan Rahoto Allah Ya Nisanta Manzon Allah{S.A.W.W} Da Kafirai Duk Nasabar Manzon Allah{S.A.W.W} Ba Kafiri Tun Daga Annabi Adam{A.S} Har Zuwa Abdullah{A.S} Har Karshen Duniya Allah Ya Tsarkakeshi Da Zuriyarsa. Wannan Tarihin Karyane!Karyane!! Karyane!!!

    1. Masha Allah. To amma Allah yasa ka karanta abinda muka wallafa, Domin ta hakane zaka fahimci abinda malamin ya fada.

      Sannan kuma ya muna fata zaka zurdafa bincike kamar yanda yayi, domin ka tabbatar da gaskiyar maganar sa ko kuma akasin haka.

      Mun gode. Da fatan zakaci gaba da kasancewa da wannan shafin.

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button