Addini

Bidiyo: Babu wanda yake raba kan Musulmai sai Malamai. Inji Dr. Sani Sharif.

Fitaccen malamin Addini Shek Dakta Sani Sharif Umar Bichi yace malamai ne Ummul aba’isin na rabuwar kan Musulmai.

Hakika raba kawunan mutane babbar matsala ce, bama a iya Addini kadai ba, harda zamantakewa. Saboda daga rabuwar kai ake samun kowacce irin ‘baraka.

Shek Sani yace Malamai sune wadanda ake sauraron su a koda yaushe, amma kuma kowanne malami yanada irin tasa fahimtar da kuma aƙida ta Addini.

Malamin ya ƙara da cewa a haka kuma kowanne malami so yake kowa ya saurare shi ya kuma bishi akan irin fahimtar tasa.

Hakika wannan maganar da Malamin ya kawo tanada matukar mahimmanci.

Ga kuma bidiyon malamin nan ƙasa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button