Labaran Kannywood

Bidiyo: Iskanci yaci uban na baya. Ado Gwanja da Mr. 442, zasu fitar da sabuwar wakar Asosa.

Lallai wannan fa shi ake kira “an gudu ba’a tsira ba”. Ado Gwanja da mai gidan Safara’u wato Mr. 442, suna shirin fitar da sabuwar wakar Chass Asosa.

Mawakan dai zasu fitar da salon wakar da a Turance ake cewa “Remix”. Wato maimaita salon wakar da aka riga akayi a baya.

Sai dai kuma iskancin da Mr. 442 yayi akan wannan sabuwar, yafi ƙarfin na Gwanja.

Domin shi Gwanja a cikin wakar da ya fitar cewa yake “Baya na nayi mini ciwo, Asosa”.

To amma shi 442 a nashi salon cewa yayi ba bayan sa ne yake masa ciwo ba, gaban sa ne. Sannan kuma duk wanda yake fahimtar yaren Hausa, idan akace “gaba” to yasan abinda ake nufi.

Bari dai ku gane wa idanun ku wannan al’amari, ga cikakken rahoton nan a ƙasa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button