Labaran Duniya

Dan ƙasar Chaina ya kashe wata Bahaushiya a Kano, saboda kishi.

Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 10 na daren ranar Juma’a bayan wanda ake zargin ya kawo wa marigayiyar ziyara, mai suna Ummakulsum Sani Buhari, a gidan iyayenta da ke kusa da ofishin Hukumar Kula da Muhalli ta Kasa (NESREA).

Wani makwabcin marigayiyar Abubakar Mustapha ya shaida wa manema labarai cewa ita bazawara ce kuma wadda ake zargin saurayinta ne.

“Lamarin ya faru ne da misalin karfe 10:00 na daren jiya. Wanda ya kashe ta saurayinta ne tun kafin ta yi aure. Mijinta ya sake ta suka ci gaba da zumunci a matsayin saurayi da budurwa. An garzaya da zuwa asibitin UMC Zhair wanda bai fi kilomita daya da gidansu ba kuma ta rasu kafin a isa.” 

Khaleed yayanta ne ya hana ’yan iskan da suka afkawa wanda ya yi kisan a lokacin da ya dawo daukar momotarsa, saboda a tunaninsa (Khaleed) zai haifar da wani abu na daban. Daga nan aka kama mutumin, aka mika shi ga ‘yan sanda,” in ji Mustapha.

Wani makwabci mai suna Muhammad Sani ya shaida wa daya daga cikin ‘yan jaridarmu cewa wanda ake zargin ya taba yunkurin kashe kansa saboda budurwar amma da ‘yan sanda suka shiga tsakani aka sasanta lamarin.

Lokacin da za ta yi aure, ya taba yunkurin kashe kansa saboda kaunar da yake mata har sai da ‘yan sanda suka shiga tsakani kuma komai ya daidaita,” in ji shi.

Ya kara da cewa an kai wanda ake zargin zuwa ofishin ‘yan sanda da ke unguwar Dorayi.

Marigayiyar, Ummakulsum wadda aka fi sani da ‘Ummita’ ta yi makarantar koyon aikin jinya da ungozoma ta Kano.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da faruwar lamarin, ya kuma yi alkawarin bayar da karin bayani daga baya.

Rahoton Fadeelah Omar Abdulmalik.

Jarida Radio.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button