Labaran Duniya

Bidiyo: Yar ƙasar Chaina mazauniyar jihar Kano tayi magana akan kisan Ummita.

Fitacciyar yar ƙasar Chainan nan wadda take zaune a Kano, kuma take furta yaren Hausa tamkar Bahaushiya tayi magana akan kisan Ummita.

Baiwar Allahn mai suna Kande, ta bayyana ra’ayin ta akan wannan aika-aika da Dan ƙasar su ya aikata, wanda ya kashe Budurwar sa mai shekaru 22, wadda ta kasance Bahaushiya yar asalin jihar Kano mai suna Ummu Kulsum, wadda ake wa lakabi da Ummita.

Wanda kuma dan Chainan mai shekaru 47, ya kashe Ummita ne ta hanyar caccaka mata wuka har saida yaga bata numfashi, kuma ya aikata hakan ne bayan ya kutsa kai har cikin gidan su Ummita ya same ta a dakin ta, sannan ya aiwatar da wannan mummunan aiki.

To a halin yanzu dai Hukumar Yansanda ta jihar Kano tuni tayi ram da wannan mutumi, kuma maganar tana Shalkwatar Yansanda dake Bompai ana ci gaba da bincike.

To yanzu dai itama ‘yar ƙasar Chaina wadda take a Kano mai suna Kande Gao, tayi magana akan wannan rashin imani.

Ga kuma bidiyon labarin nan a ƙasa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button