Labaran Duniya

Bidiyo: Dan ta’adda Bello Turji ya aika wa Sojojin Nigeria zazzafan gargadi.

Gawurtaccen ‘Dan bindigar nan, wanda ya addabi Arewacin Najeriya musamman bangaren jihar Zamfara da jihar da Sokoto mai suna Bello Turji, ya aika wani zazzafan sako zuwa ga Sojojin kasar.

Turji ya aika sakon ne bayan abinda ya faru a cikin satin da ya gabata, na luguden wuta da Sojojin sukayi a cikin wani Daji dake yankin Shinkafi a jihar Zamfara. Inda kuma wannan guri, shine inda Bello Turji da mutanen sa suke fakewa.

Harin yayi sadaniyyar mutuwar wasu guggun yan ta’adda daga cikin mutanen Turji, dalilin da yasa ya koka akan lamarin har aika wannan sako.

Ga bidiyon cikakken rahoton nan a kasa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button