Labaran Kannywood

Bidiyo: Yanda mutuwar Yakubu Kafi Gwamna ta jijjiga ‘yan Kannywood.

Allahu Akbar, a jiya Talata ne dai masana’antar Kannywood tayi wani babban rashi wanda baza’a iya mantawa dashi ba, wato na mutuwar tsoho, kuma fitaccen jarumi a masana’antar mai suna Malam Umar Yahaya Manumfashi wanda akafi sani da Bankaura.

Bankaura dai shine jarumin da yake amsa sunan “Yakubu Kafi Gwamna” a cikin shirin nan mai dogon zango, wanda ake haskawa a gidan Talabijin na Arewa24 wato Kwana 90.

Tsohon jarumin ya fara harkar fim tun daga Diramar Dabe, wato “Stage Drama” Ma’ana tun kafin a kirkiri masana’antar Kannywood.

Kafin rasuwar sa, yasha fama da rashin lafiya, inda aka bashi Gado aka kwantar dashi a wani Asibiti dake unguwar Hausawa a jihar Kano, mai suna Pinnacle Special Hospital.

Hakika wannan mutuwa tayi matukar jijjiga ‘yan masana’antar ta Kannywood.

Ga kuma bidiyon cikakken rahoton nan a kasa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button