Labaran Kannywood

Bidiyo: Rahma Sadau ta ƙaryata wani labari da aka wallafa akan ta.

Fitacciyar jarumar Kannywood da Nollywood da kuma Bollywood wato Rahma Sadau, ta ƙaryata wani labari da wani gidan jarida suka wallafa akan ta.

Jarumar tayi ƙorafi, inda tace ko kadan batada wata masaniya akan wannan labari.

Labarin kuma da aka yada akan jarumar shine, ance wai tana cikin jerin matan Kannywood, wadanda aka zaba domin tallata takarar Bola Ahmad Tinubu. Inda Rahma tace, wannan ba komai bane face tsantsar zuƙi ta malle.

To abinda dai Rahma take zargi shine wani ya karbi kudi da sunan ta, ba tare da sanin ta ba.

Rahma dai ta wallafa wannan al’amari ne domin shi Bola Tunubun ya san halin da ake ciki. Ga dai cikakken labarin nan a ƙasa.

Related Articles

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button