Siyasa

Buhari yace a cikin alkawuran da ya ‘daukar wa ‘yan Najeriya, babu wanda bai cika ba.

Tofa! Shugaban ‘kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya kawo wata magana wadda ‘yan kasar suka bude shafin cecekuce akai.

Inda shugaban yace duk alkawuran da ya ‘daukar wa ‘yan Najeriya a lokacin da ya karbi mulki babu wanda bai cika ba.

Jama’a da dama dai sunji matukar mamakin wannan magana ta shugaba Buhari, duba da yanda suke kallon ‘kasar a matsayin wadda batada makama, komai ya lalace.

Buhari dai yayi wannan jawabi ne a ranar da Najeriya take murnar cika shekaru 62 da samun ‘yancin kai.

Shugaban kasar yace Gwamnatin tayi hubbasa, tayi ƙoƙari sosai wajen habaka da bunkasa tattalin arzikin ƙasar, da kuma tantance bayanai akan asusun ajiyar banki na yan ƙasar.

Haka zalika yace Gwamnatin tayi matukar ƙoƙari wajen bunkasa aikin Gona, wanda hakan ya janyo wa ƙasar gagarumar nasara. Inda yace duk wannan sun faru ne a ƙarƙashin mulkin sa.

Sai dai shugaban yace yana jin matukar ciwo da takaici, akan yajin aikin da ƙungiyar malaman jami’o’i na Najeriya suke yi, wanda a yanzu sun shafe sama da watanni 7 sunayi.

Buhari yace a bangaren makarantun jami’o’i yayi tsare-tsare masu ingancin gaske, wanda a cikin shekaru 11 da suka wuce ba’a taba yin irin su ba, shiyasa yace bai taba tsammanin wannan yajin aikin zai faru ba.

Daga ƙarshe shugaban ya sake jaddada aniyar sa ta cewa zaiyi duk mai yiwuwa, domin ganin cewa an gudanar da sahihin zabe a shekara mai zuwa ta 2023.

To sai dai wannan jawabi na Buhari zamu iya kiran sa da jawabin Bankwana, domin kuwa shekara bazata dawo ta riske shi akan mulki ba. Kasancewar ya gama wa’adin sa na shekara 8, kamar yanda Kundin tsarin mulkin Najeriya ya tabbatar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button