Labaran Duniya

Bidiyo: ‘Dan Chainan da ya kashe Ummita ya raina wa Dokar Nigeria hankali a Kotu.

Tofa! ‘Dan ‘kasar Chainan mai suna Mista Geng Quanrong wanda ya kashe Budurwar Bahaushiya wato Ummulkhairi Sani, yazo da rainin hankali a Kotu.

Quanrong dai ana zargin sa ne da kashe masoyiyar sa, wadda ta kasance Bahaushiya ‘yar asalin jihar Kano, unguwar Janbulo.

Kuma ya kashe ta ne ta hanyar caccaka mata wuka, kamar yanda rahotanni suka tabbatar.

Sai dai Dan Chainan yazo da wani rainin hankali a Kotu, a yayin zaman shara’ar da akayi na ranar Alhamis ‘din da ta gabata.

Inda yaki zuwa Kotun tare da Lauyan da zai kare shi, duk da yasan cewa shara’ar bazata yiwu idan babu lauya ba, kasancewar zargin da ake masa ba ‘karamin al’amari bane, tunda har ya shafi kisan kai.

Tashar Sabuwar Rayuwa, ta shirya mana cikakken rahoton. Ga bidiyon nan ‘kasa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button